Connect with us

News

Jami’an ’Yansanda Sun Ceto Yaro Ɗan Shekara 2 Da Aka Yi Garkuwa Shi A Kano

Published

on

Screenshot 2026 04 25 080733

Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta ce ta ceto wani ƙaramin yaro mai shekara biyu da aka sace a jihar, tare da kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin.

Haka kuma rundunar ta ce ta kwato Naira 930,000 daga cikin kuɗin fansa da iyalan yaron suka biya.

Advertisement

Farfesa Abdalla Uba Adamu Ya Yi Ritaya Daga Jami’ar Bayero Kano Bayan Shekaru 46 Na Aiki

‎Ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar, ya ce an samu nasarar ne sakamakon sahihan bayanan sirri da kuma bincike mai zurfi.

Advertisement

‎A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Afrilu a unguwar Gwammaja da ke ƙaramar hukumar Dala, inda wani mazaunin yankin ya kai rahoton sace ɗansa, Aliyu Muhammad, mai shekara biyu, a gaban gidansu.

‎’Yan sanda sun ce bayan sace yaron, masu garkuwa da shi sun tuntubi iyayinsa, inda suka nemi kuɗin fansa na Naira miliyan ɗaya, wanda daga bisani aka biya. Sai dai duk da karɓar kuɗin, ba su saki yaron ba.

Advertisement

‎Bayan samun rahoton, kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya umarci sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane da su fara aiki cikin gaggawa.

‎Sanarwar ta ce ta hanyar ci gaba da bincike da amfani da dabarun fasaha, jami’an tsaro sun gano maboyar waɗanda ake zargin tare da cafke su.

Advertisement

‎An bayyana sunayen waɗanda ake zargin da Hassan Umar, Abdullahi Hamisu da Hussaini Saminu, duk daga unguwar Gwammaja, inda aka tsare yaron.

‎’Yan sanda sun ce an samu nasarar ceto yaron cikin ƙoshin lafiya daga gidan Hussaini Saminu, sannan aka mayar da shi wajan iyayinsa.

Advertisement

‎Haka kuma an kwato Naira 930,000 daga hannun waɗanda ake zargin, a matsayin wani ɓangare na kuɗin fansar da aka biya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending