Sports
Karon Farko Cikin Shekaru 20, Arsenal Ta Kai Wasan Ƙarshe A Champions League
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta tsallake zuwa zangon wasan ƙarshe na gasar Zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA Champions League, bayan doke Atletico Madrid da ci 1 da nema a wasan dab da na ƙarshe na biyu.
An tashi wasan farko ne 1 da 1 a gidan Atletico Madrid a makon da ya gabata.
Ƙalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
Wannan na nufin Arsenal za ta haɗu Paris Saint Germain ko kuma Bayern Munich a wasan na ƙarshe domin neman lashe kofin na 2026.
A shekarar 2006 ne Arsenal ta kai wasan ƙarshe a gasar, inda a lokacin ne ta rasa damar lashe kofin bayan kayen da ta sha a hannun Barcelona da ci 2 da 1.
Daga cikin ƙungiyoyin da suka rage a gasar, Bayern ta lashe kofin sau shida, PSG ta ɗauka sau ɗaya yayin da Arsenal ke cigaba da harin samun na farko tun bayan fara gasar shekaru sama da sittin da suka gabata.
