News
An Samu Sama Da Mutum 100 Da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Sankarau A Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa an samu mutum 105 da ake zargin sun kamu da cutar sankarau a kusan ƙananan hukumomi 20 na jihar, lamarin da ya zo daidai lokacin da ake fama da matsanancin zafi a sassan jihar.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Katsina (PHCDA), Dakta Shamsuddeen Yahaya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Katsina.
Jamhuriyar Nijar Na Son Ƙara Adadin Jihohinta Daga 8 Zuwa 19 Da Kuma Sauya Sunayen Wasu Jihohin
Ya ce har yanzu ba a tabbatar da bullar cutar ta hanyar gwaje-gwaje ba, amma ana ɗaukar duk masu alamun cutar cikin gaggawa domin ba su kulawar lafiya da sanya ido a kansu.
A cewarsa, alamomin da ake lura da su sun haɗa da Curar na kawo zafin jiki wanda daga baya yakan iya zama Zazzabi da Sankarewan wuya, waɗanda ke daga cikin manyan alamomin cutar sankarau.
Dakta Shamsuddeen ya ce wasu ƙananan hukumomi sun fi fuskantar yawaitar masu alamun cutar, inda ya ambaci Kafur da Zango da Dutsi da Musawa da sauran yankuna a matsayin wuraren da abin ya fi kamari.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙara tsaurara matakan sa ido da ɗaukar matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, inda aka kunna Cibiyar Ayyukan Gaggawa (EOC) mai aiki sa’o’i 24 domin jagorantar ayyukan daƙile cutar tare da haɗin gwiwar jami’an lafiya da abokan hulɗa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta riga ta tanadi magunguna da kayan aikin lafiya a manyan cibiyoyin lafiya tun kafin bullar lamarin, domin tabbatar da fara jinya cikin gaggawa ga duk wanda aka gano da alamun cutar.
