News
Harkar Tsaro Ta Taɓarɓare A Mulkin Gwamna Abba — Gwarzo
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Jihar Kano kuma tsohon mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Da yake zantawa da BBC Hausa, Gwarzo ya ce matsalar tsaro a Kano na ƙara muni, inda ake ci gaba da fuskantar kashe-kashe, sace-sacen mutane da hare-hare a wasu ƙananan hukumomi na jihar.
Ya ce garuruwan Tsanyawa, Shanono da Gwarzo sun sha fama da hare-hare akai-akai, inda aka kashe mutane, aka kwashe dukiyoyi, sannan wasu kuma aka yi garkuwa da su.
“A Tsanyawa, an kashe mutane da dama, an kuma kwashe dukiyoyinsu. Haka abin ya faru a Shanono, har zuw Gwarzo. ’Yan bindiga na kai hare-hare, suna kashe mutane, wasu kuma an yi garkuwa da su sama da watanni shida,” in ji shi.
Ya kuma ce har a birane ma an kashe mutane a ’yan kwanakin nan.
“Allah ne kaɗai ya san yawan mutanen da aka kashe cikin makonni uku da suka gabata. Ana kisan kai-tsaye. Ina zaman lafiyar yake?” in ji shi.
Gwarzo ya zargi yadda aka kashe wasu mutane a ranar rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar.
“A ranar da aka rantsar da mataimakin gwamna, an kashe mutane biyar. Daga baya kuma wani ya rasu, wanda adadin ya kai shida. Ina tsaro?” in ji shi.
Ya kuma soki shirin gwamnatin jihar na “Kano First”, yana mai cewa bai kawo ci gaba a fannin tsarokamar yadda aka alƙawari.
“Idan ka zo Kano, za ka ji ana cewa ‘Kano First’ na nufin haɗin kai tsakanin shugabanni, amma tun da aka fara shi, matsalar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa,” in ji shi.
Gwarzo ya ce gwamnatin jihar ta kasa cika alƙawarin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’umma.
