News
Wasu Ƴan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Janar Mai Ritaya Da Matarsa A Katsina
Rahotanni daga ‘yan sanda da jami’an tsaro a Katsina na bayyana sace tsohon kakakin rundunar tsaro,janar mai ritaya Rabe Abubakar, da matarsa a Jihar Katsina.
Janar mai ritaya da matarsa na kan hanyarsu ta zuwa Katsina a jiya Asabar lokacin da ‘yan bindiga suka tare motarsu a Karamar Hukumar Matazu suka kuma tafi da su bayan musayar wuta,inda aka bayyana cewa direban su ya samu rauni.
Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutane 37, Sama Da 3,000 Sun Kamu A Borno
Abubakar Aliyu, Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Katsina, ya tabbatar da lamarin ga PREMIUM TIMES a jiya Asabar da yamma, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara aikin bincike da nufin ceto su.
Motar tsohon janar ta kama hanya da misalin karfe 11 na dare,ƴan bindiga suka tare motar tare da bude wuta,daga bisani suka kuma yi awon gaba da su,yayin da direban ya tsere.
Da samun labarin, Kwamishinan ƴansanda ya ziyarci wurin don tantance wadanda abin ya shafa a wurin kuma ya tura karin rundunonin tsaro da kayan aiki don tallafawa kokarin ceto.
An baza jami’an tsaro, ciki har da ƴan sa kai, suna kan aikin bincike da ceto, suna kewaye da dazuzzukan da ke yankin. Wasu bayyanai daga yankin na nuni da cewa, harin ya faru ne kusa da ƙauyen Aduwa, kafin Karaduwa, inda aka ruwaito cewa ‘yan bindigar sun bude wuta kan motar.
Majiya ta ce direban ya samu rauni a harbin bindiga amma ya tsira. Da farko an kai shi wani babban asibitin kula da lafiya a Matazu kafin a mayar da shi Katsina don ci gaba da jinya.
