Connect with us

News

An Samu Ƙarin Mutum 274 Da Suka Kamu Da Cutar Kwalara Cikin Sa’o’i 24 A Borno

Published

on

Annobar cutar kwalara na ci gaba da yaduwa a Jihar Borno, inda aka samu karin mutum 274 da suka kamu da cutar cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya daga adadin wadanda suka harbu zuwa 4,204 a kananan hukumomi 10 na jihar.
Manajan Sashen Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) ta jihar, Dakta Jacob Thlizer, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya da dakile yaduwar cutar da aka gudanar a Maiduguri.
Ya ce ya zuwa yanzu mutum 39 sun rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar, yayin da aka tabbatar da kamuwar mutane a gundumomi 36 da ke cikin yankunan da annobar ta shafa.
A cewarsa, kananan hukumomin da aka samu bullar cutar sun hada da Jere, Bama, Kaga, Mafa, Kwaya Kusar, Maiduguri, Konduga, Monguno, Magumeri da Ngala.
Thlizer ya bayyana cewa Maiduguri ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar da mutum 2,404, sai Jere mai mutum 1,214, Konduga 275, Mafa 184, Monguno 90, Kaga 18, Bama takwas, Kwaya Kusar takwas, Ngala biyu, yayin da Magumeri ke da mutum guda da ya kamu da cutar.
Ya ce gwamnatin jihar ta kaddamar da matakan gaggawa domin dakile yaduwar annobar, ciki har da wayar da kan al’umma a wuraren da cutar ta fi kamari, hada gwiwa da abokan hulda a bangaren lafiya da kuma samar da kayayyakin aikin da ake bukata.
Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jama’a ta Jihar Borno, Alhaji Shettima Muhammad, ya ce gwamnati ta samar da cibiyoyin kula da masu fama da cutar domin tabbatar da cewa marasa lafiya suna samun kulawar gaggawa.
Ya bayyana cewa an ware cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa da ke Njimtilo tare da samar da sansanin kula da masu fama da kwalara mai dauke da gadaje sama da 1,000 a Ngarannam domin karbar masu jinya.
A nasa bangaren, Sakataren Gwamnatin Jihar Borno, Alhaji Bukar Tijani, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da bai wa bangaren lafiya dukkan goyon bayan da ya dace domin dakile yaduwar cutar.
Ya kuma bukaci jami’an lafiya da sauran masu ruwa da tsaki su rika sanar da gwamnati cikin gaggawa duk wata matsala da za ta iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na shawo kan annobar.
Kokarin hukumomi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda cutar ke kara yaduwa a wasu sassan jihar, lamarin da ya sa ake kira ga al’umma da su kara himma wajen kiyaye tsafta da amfani da ruwa mai tsafta domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

AMINIYA

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending