Connect with us

News

“Ba Za Mu Amince Da Katsalandan Ba” — ADC Kano Ta Tabbatar Da Ibrahim Khalil A Matsayin Ɗan Takarar Gwamna

Published

on

IMG 20260621 114543 052

Shugabannin riƙon ƙwarya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Kano tare da manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun sake tabbatar da Malam Ibrahim Khalil a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar domin zaɓen shekarar 2027.

Sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Sakatariyar ‘Yan Jaridu ta Jihar Kano, inda suka yi kira ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya mutunta sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 22 ga Mayu, 2026.

Advertisement

INEC Ta Ayyana Abiodun Oyebanji A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Ekiti

Da yake jawabi a madadin shugabannin jam’iyyar, tsohon shugaban ADC na Jihar Kano, Alhaji Musa Shu’aibu Ungogo, ya ce Malam Ibrahim Khalil ne ya samu nasara a zaɓen fidda gwani bayan samun kuri’u 55,851, yayin da abokin hamayyarsa ya samu kuri’u 4,000 kacal.

Advertisement

Ya ce sakamakon zaɓen ya nuna irin amincewar da mambobin jam’iyyar suka bai wa Ibrahim Khalil, yana mai jaddada cewa babu wani dalili da zai sa a yi ƙoƙarin sauya ra’ayin da masu zaɓe suka bayyana.

“An gudanar da zaɓe cikin adalci kuma an samu wanda ya yi nasara da wanda ya sha kaye. Don haka wajibi ne a mutunta sakamakon da aka samu domin kare martabar jam’iyyar da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya a cikin gida,” in ji shi.

Advertisement

Alhaji Musa Ungogo ya bayyana cewa Kano na da muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, musamman a Arewa maso Yamma, saboda haka jam’iyyar na buƙatar ɗan takarar da ke da karɓuwa a tsakanin al’umma.

A cewarsa, Ibrahim Khalil na da farin jini a tsakanin matasa, mata da malamai, kuma ya dade yana taka muhimmiyar rawa wajen gina jam’iyyar ADC tun daga kafuwarta a jihar.

Advertisement

Shugabannin jam’iyyar sun kuma yi Allah-wadai da abin da suka kira katsalandan daga wasu jami’an jam’iyyar na ƙasa cikin harkokin reshen Kano.

Sun yi zargin cewa wasu na ƙoƙarin yin tasiri a kan sakamakon zaɓen fidda gwani duk da cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar bai ba su irin wannan iko ba.

Advertisement

“Ba za mu amince da katsalandan a harkokin jam’iyyar a Kano ba. Mambobin jam’iyyar ne suka zaɓi wanda suke so ya wakilce su, kuma dole ne a mutunta wannan zaɓi,” in ji sanarwar.

Har ila yau, shugabannin sun yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa ƙarancin kuɗi ka iya zama cikas ga takarar Ibrahim Khalil, suna masu cewa tarihin siyasar Kano ya nuna cewa masu zaɓe kan fifita mutunci, nagarta da gaskiya fiye da ƙarfin kuɗi.

Advertisement

Sun bayyana cewa jam’iyyar ADC a Kano ta haɗu tsaf wajen mara wa Ibrahim Khalil baya, tare da kira ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya ɗauki matakan da suka dace domin dakile duk wani yunƙurin da zai iya haddasa rikici a cikin jam’iyyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending