Connect with us

News

Kwamitin CVR Na Kano Ya Haɗa Gwiwa Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Don Ƙara Yawan Masu Rajistar Katin Zaɓe

Published

on

IMG 20260627 072001 790
Advertisements
ads

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a Jihar Kano sun sake jaddada aniyarsu ta mara wa gangamin Rajistar Masu Zaɓe Ta Dindindin (CVR) baya, tare da yin kira ga ma’aikata da sauran ‘yan ƙasa masu cancantar kaɗa ƙuri’a da su yi rajista domin samun Katin Zaɓe na Dindindin (PVC).

An bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da Ƙaramin Kwamitin Ƙwadago na Kwamitin Aikin Rajistar Masu Zaɓe Ta Dindindin (CVR) na Jihar Kano ya shirya, domin ƙarfafa gwiwar ma’aikata su shiga aikin rajistar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke gudanarwa.

Kwalliya ta biya kuɗin sabulu: Mahalarta taron ASCON sun yabawa masu shirya taron bisa kulawa ta musamman da suke ba su.

Da yake jawabi a taron, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), reshen Jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa, ya ce ma’aikatan jihar sun shirya tsaf wajen tabbatar da nasarar aikin rajistar masu zaɓe, yana mai bayyana hakan a matsayin wata muhimmiyar gudunmawa ga bunƙasar dimokuraɗiyya.

Ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Jihar Kano za ta taimaka wajen ƙarfafa al’umma su shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya ta hanyar yin rajista da kuma mallakar katin zaɓe.

“Ina kira ga dukkan ma’aikata su sauke nauyin da ya rataya a kansu na ɗan ƙasa ta hanyar yin rajista da kuma samun Katin Zaɓe na Dindindin, domin shi ne sahihin makamin zaɓar shugabannin da suke so,” in ji shi.

Advertisement

Tun da farko, Sakataren Ƙaramin Kwamitin Ƙwadago, Kwamared Usman Bello, ya bayyana cewa aikin rajistar masu zaɓe na da matuƙar muhimmanci wajen faɗaɗa damar al’umma ta shiga cikin tafiyar mulki da kuma ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya.

Ya sanar da cewa an tanadi cibiyar rajista ta musamman a harabar Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kano, inda za a yi wa ma’aikata da iyalansu rajista daga ranar Litinin, 29 ga Yuni zuwa Juma’a, 4 ga Yuli, domin sauƙaƙa musu gudanar da aikin.

Shi ma Shugaban Ƙaramin Kwamitin Ƙwadago, Kwamared Abbas Ibrahim, ya bayyana rajistar masu zaɓe a matsayin haƙƙi da kuma nauyin da ya rataya a kan kowane ɗan ƙasa mai cancantar kaɗa ƙuri’a.

Ya ce kwamitin ya tsara ingantattun dabarun wayar da kai domin tabbatar da cewa babu wani ma’aikaci ko ɗan ƙasa mai cancanta da zai rasa damar yin rajista.

Kwamared Abbas ya tunatar da mahalarta taron cewa wa’adin rajistar masu zaɓe zai ƙare a ranar 10 ga Yuli, bayan haka kuma za a fara baje kolin kundin masu zaɓe domin karɓar ƙorafe-ƙorafe da gyaran bayanai.

Ya buƙaci ma’aikata da iyalansu da su yi amfani da sauran kwanakin da suka rage wajen yin rajista ko sabunta bayanansu kafin wa’adin ya cika.

Advertisement

An kammala taron da zaman tattaunawa, inda mahalarta suka nuna cikakken goyon bayansu ga gangamin wayar da kai tare da alƙawarin ƙarfafa sauran ma’aikata su shiga aikin rajistar masu zaɓe.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending