News
Saraki Ya Ɗauki Nauyin Ragowar Kuɗin Karatun Ɗalibar UNILORIN Mai First Class Zuwa Italiya
Tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi alƙawarin zai ƙarasa biyan kuɗin da suka rage ga ɗalibar nan wadda ta karanta fannin lissafi a jami’ar Ilorin, wato Adisa Blessing Oluwafikayo, wadda ta samu tallafin karatu (scholarship) domin ta je ta yi digiri na biyu a wata jami’a a ƙasar Italiya.
Saraki ya yi alƙawarin ne ta shafinsa na X bayan ya ci karo da rubutun da ɗalibar ta yi tana neman taimako a wajen jama’a domin ta ƙarasa biyan kuɗin wajen zama da ragowar tsarabe-tsarabe da ake buƙata.
Wasu Bata Gari Sun Hallaka Mai Gadin Asibiti, Sun Sace Kayan Sola A Kano
A rubutun da ta yi a shafin na ta, Adisa Blessing Oluwafikayo ta ce:
” Ku taimaka min na cika burina”
“Sunana Adisa Blessing Oluwafikayo, na kammala digiri na farko a jami’ar Ilorin kuma na fito da daraja ta farko wato first class”
“Na samu tallafin karatu a wata jami’a a ƙasar Italiya domin yin digiri na biyu amma ina bukatar kuɗaɗen da zan yi amfani da su wajen inda zan zauna idan na je da ragowar tsarabe-tsarabe”
Nan take Saraki yaga rubutun na ta kuma ya yi mata martani kamar haka:
“Zuwa ga Adisa, yanzu naga abin da kika rubuta a shafin X kuma na yi farin ciki musamman ganin kin gama da First Class a fannin lissafi a jami’ar Ilorin kuma kika samu tallafin karatu a ƙasar Italiya, tabbas wannan nasara ce babba.
Saraki ya ci gaba da cewa, “Babu wani matashi a ƙasar nan da zai yi aiki tukuru irin naki kuma ya samu wannan damar a bari ta kuɓuce saboda rashin kuɗi. Na yi alƙawarin zan biya duka kuɗaɗen da ake buƙata. Ina miki fatan alheri, ki je ki ci gaba da zama jakada ta gari ga Nigeriya.
Ba wannan ne karo na farko ba da Saraki yake ɗaukar nauyin karatun matasa a ƙasar nan inda duk shekara yana ɗaukar nauyin ɗalibai a jihar Kwara da ragowar sassan ƙasar nan.
