Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Kotun Tafi-da-Gidanka Kan Masu Laifin Miyagun Ƙwayoyi

Published

on

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai tsaye Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin kafa Kotun Tafi-da-Gidanka domin gaggauta sauraren shari’o’in da suka shafi miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan zamantakewa a jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Meta Da X Kan Amfani Da Labaran Najeriya

Sanarwar ta ce kafa kotun zai taimaka wajen hanzarta gudanar da shari’a, tabbatar da adalci cikin lokaci, da kuma ƙarfafa bin doka da oda. Ta kuma ce matakin zai zama darasi ga masu aikata irin waɗannan laifuka.

A cewar sanarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi, wadda ke yin illa ga al’ummar jihar, musamman matasa.

Gwamnan ya kuma umarci kwamitin kar-ta-kwana da gwamnatin jihar ta kafa kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ya ƙara ƙaimi tare da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da nasarar yaƙin da ake yi da shaye-shaye da sauran laifukan da ke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending