Connect with us

News

Kotun Filato Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa

Published

on

IMG 20260711 WA0010

Rikicin da ya shafi bayar da shaidar zama ɗan ƙasa a Ƙaramar Hukumar Jos North ta Jihar Filato ya ɗauki sabon salo, bayan da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jos North, ƙarƙashin jagorancin Ujah Anaguta, Mai Martaba Pozoh Johnson, tare da Ƙungiyar Cigaban Anaguta (Anaguta Development Association) da wasu ƙungiyoyi suka nemi Babbar Kotun Jihar Filato ta ba su damar shiga cikin shari’ar da ke tsakanin Fatima Baba Akawu da Ƙaramar Hukumar Jos North.

A zaman kotun da aka gudanar ranar Juma’a, lauyoyin ɓangarorin biyu sun yi muhawara kan buƙatar masu neman shiga cikin shari’ar. Lauyoyin nasu sun ƙalubalanci halascin bayyanar wasu manyan lauyoyi masu mukamin SAN da ke wakiltar mai ƙara, suna masu cewa ba su kasance cikin shari’ar tun daga farkonta ba, kuma babu wata takardar da ta nuna an sauya lauyan da ya fara gudanar da karar.

Sai dai lauyoyin ɓangaren mai ƙara da na Ƙaramar Hukumar Jos North sun yi fatali da waɗannan hujjoji, inda suka gabatar wa kotu da dalilai da tanade-tanaden doka da suka ce sun tabbatar da sahihancin matsayinsu.

Bayan sauraron hujjojin kowane ɓangare, Alƙalin Babbar Kotun Jihar Filato, Mai Shari’a Justice C. Donglong, ya ɗage yanke hukunci kan buƙatar shiga cikin shari’ar zuwa ranar 29 ga Oktoban 2026.

A cikin ƙudurin da Ƙaramar Hukumar Jos North ta gabatar a gaban kotu, ta nemi a soke hukuncin da aka yanke ranar 9 ga Yunin 2026, tana mai cewa ba a bi ƙa’idojin shari’a da suka dace ba. Karamar hukumar ta yi zargin cewa ba ta samu sahihin sammaci ko takardun sauraron ƙara ba, lamarin da ta ce ya tauye mata haƙƙinta na samun cikakken sauraro kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Har ila yau, ta bayyana cewa takardar sanarwar sauraron ƙara da aka taɓa aikewa gare ta ta fito ne daga Babbar Kotun Pankshin, alhali shari’ar tana gudana a Babbar Kotu ta 17 da ke West of Mines, inda ta ce an ci gaba da shari’ar ba tare da saninta ko wakilcinta ba.

Advertisement

Masana shari’a na ganin hukuncin da kotu za ta yanke kan wannan buƙata zai iya yin tasiri wajen ci gaban shari’ar, wadda ta shafi batun shaidar zama ɗan ƙasa a Jos North kuma ke jan hankalin al’umma a Jihar Filato.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending