News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mota Mara Lamba Da Bindiga Kirar Pistol Da Kayan Maye A Kano
Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wata mota mara lamba da ake zargin tana dauke da bindigar ƙirar pistol da kayan maye, tare da cafke wani mutum mai suna Mahe Ibrahim, mai shekaru 51, mazaunin unguwar Rijiyar Zaki, bisa zargin hannu a aikata laifuka.
Kwamishinan Ƴansandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake nuna wasu kayayyakin da rundunar ta kama ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Litinin.
Wasu Ɓata Gari Sun Hallaka Mai Sayar Da Shayi A Kano
Ya ce jami’an Ƴansanda na sashen Panshekara ne suka kama wanda ake zargin a Sabon Titin Dorayi bayan samun bayanan sirri daga mazauna yankin cewa yana ƙoƙarin satar wata mota.
A cewarsa, bayan kama wanda ake zargin, jami’an sun gano wata bindiga ƙirar pistol, wuka da kuma tabar wiwi a hannunsa, sannan suka kwato motar da ake zargin an yi yunƙurin sata, wadda ba ta da lambar rajista.
Bakori ya bayyana cewa kamen ya zo ne a daidai lokacin da rundunar ke ci gaba da aiwatar da umarnin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya na kakkaɓe motocin da ba su da lambar rajista ko kuma waɗanda aka rufe lambobinsu domin inganta tsaro da dakile ayyukan masu laifi.
Ya ƙara da cewa bincike kan lamarin na ci gaba, yana mai tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar ba za ta sassauta ba wajen binciken ababen hawa da kuma kama duk masu karya doka, yana mai shan alwashin ci gaba da jajircewa domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.
-
News6 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News7 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, Mutumin Da Ake Zargi Da Kafa Hukumar Bogi
