News
Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sa Hannu Kan Dokar Hana Daba A Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomi kan Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, tare da sanya hannu kan Dokar Zartarwa da za ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da daba da sauran ayyukan ta’addanci a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Dakarun Soji Sun Hallaka Babban Jami’in Yada Farfagandar ISWAP Abu Salim Al-Barnawi
A cewar gwamnan, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan matsalolin da ke barazana ga makomar matasan Kano, saboda yana haddasa aikata laifuka, lalata iyalai, raunana tattalin arziki da kuma kawo cikas ga zaman lafiya.
Ya ce an kafa kwamitin ne domin haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tattara bayanan sirri, yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, wayar da kan al’umma da kuma kula da masu fama da matsalar shaye-shaye.
Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar wa kwamitin duk abin da yake buƙata domin gudanar da aikinsa yadda ya kamata, ciki har da kuɗaɗen gudanarwa, motocin aiki, ofisoshi, kayan aiki da kariyar jami’an tsaro.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Kano ta riga ta kafa cibiyoyin gyaran masu shaye-shaye na maza da mata, tare da alƙawarin faɗaɗa ayyukan gyaran hali da sake dawo da masu shaye-shaye cikin rayuwar al’umma.
Game da Dokar Zartarwar da ya rattaba wa hannu, gwamnan ya ce za ta samar da ingantaccen tsarin doka da zai taimaka wajen murƙushe ƙungiyoyin daba, dakile tashe-tashen hankula masu alaƙa da siyasa da kuma bai wa hukumomin tsaro damar aiwatar da aikinsu cikin inganci.
Da yake jawabi bayan rantsar da kwamitin, shugaban kwamitin, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado, ya gode wa gwamnan bisa wannan amana da aka ɗora masa, yana mai alƙawarin gudanar da aikin cikin gaskiya, adalci da riƙon amana ba tare da nuna son kai ba.
Ya ce kwamitin zai yi aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyin ilimi da shugabannin al’umma domin magance matsalar shaye-shaye da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Kano.
Gwamna Abba ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su haɗa kai da gwamnati ta hanyar bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi da daba nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa sabuwar dokar da aka sanya wa hannu tare da ayyukan kwamitin za su taimaka wajen rage laifukan da ke da alaƙa da miyagun ƙwayoyi da daba, tare da inganta tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.
-
Opinion3 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion3 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
