News
Aƙalla Fasinjoji 68 Ne Suka Tsallake Rijiya Da Baya A Jirgin Enugu Air
Aƙalla Fasinjoji 68 da ke cikin wani jirgin saman kamfanin Enugu Air sun tsallake rijiya da baya bayan da jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Benin da ke Jihar Edo a ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce jirgin mai lambar 5N-ENR na kan hanyarsa daga Enugu zuwa Benin, kafin ya ci gaba da tafiya zuwa Legas, lokacin da lamarin ya faru.
Wata majiya daga filin jirgin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida cewa bayan jirgin ya sauka, ya kauce daga hanyar saukar jirage tare da shiga wani yanki mai ciyayi da ke gefen titin jirgin.
Nan take jami’an Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) suka isa wurin domin gudanar da aikin ceto, inda suka fitar da dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin cikin aminci.
Babu rahoton mutuwa ko samun munanan raunuka a hatsarin, yayin da hukumomin da abin ya shafa suka fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jami’an ceto suka gudanar da aikin fitar da fasinjojin daga jirgin cikin gaggawa.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
