News
INEC Ta Ce Ba Za Ta Ƙara Wa’adin Rajistar Masu Zaɓe Ba
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta sake tsawaita wa’adin rajistar masu zaɓe ba, duk da kiraye-kirayen da jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin farar hula suka yi na neman a ba da ƙarin lokaci.
Mataimakin Daraktan Sashen Wayar da Kan Masu Zaɓe da Hulɗa da Jama’a na INEC, Wilfred Ifogah, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce matakin ya zama dole domin bai wa hukumar damar kammala sauran shirye-shiryen gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.
“Kada Wani Ɗan Siyasa Ya Zo Wajena Yana Neman A Saki Ɗan Daba Idan Muka Kama Shi ” — Rimin-Gado
Ifogah ya ce duk da cewa wasu ‘yan ƙasa ba su samu damar kammala rajistarsu ba, hukumar ba za ta iya ci gaba da aikin rajistar ba saboda ƙuntataccen lokacin da ya rage kafin fara wasu muhimman matakai na shirye-shiryen zaɓe.
“Dole ne mu kawo ƙarshen aikin rajista a wannan lokaci. Muna ba da haƙuri ga waɗanda ba su samu damar kammala rajistarsu ba, amma a halin yanzu babu damar ci gaba da aikin,” in ji shi.
Ya tunatar da cewa INEC ta riga ta amince da tsawaita wa’adin rajistar na makonni biyu bayan koke-koken masu ruwa da tsaki, kafin daga bisani ta rufe aikin kamar yadda jadawalinta ya tanada.
A cewarsa, tsawaita wa’adin da aka yi tun farko ya ƙara wa hukumar nauyin aiki, domin yanzu tana da alhakin tattara bayanan rajista, tantance su, da kuma gyara duk wata matsala kafin fitar da kundin masu zaɓe na ƙarshe.
Ifogah ya bayyana cewa INEC na buƙatar fiye da kwanaki 75 bayan rufe rajista domin gudanar da cikakken tantancewa da gyaran bayanan masu rajista kafin fitar da sahihin kundin masu zaɓe da za a yi amfani da shi a babban zaɓen shekarar 2027.
Hukumar ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tanadin Dokar Zaɓe da jadawalin da ta fitar, domin tabbatar da an gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya, adalci da kuma ingantaccen shiri.
