News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 5 Bisa Zargin Samar Da Jabun Magungunan Gargajiya A Kano
Rundunar ƴan sandan shiyya ta ɗaya a Kano ta kama mutane biyar bisa zargin yin kwaikwayon wani likitan magungunan gargajiya da kuma samarwa, siyarwa da rarraba magungunan gargajiya na jabu da sunansa.
An kama waɗanda a ke zargin ne bayan rundunar ta karɓi ƙorafi daga Dakta Abdulwahab Abubakar Goni Bauchi, shugaban Dr. Abdulwahab Abubakar Herbal and Islamic Clinic da ke Bauchi
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 10 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Jigawa
Ya zargi mutanen da yin amfani da sunansa, hoton kasuwancinsa da karatunsa wajen tallata tare da sayar da jabun magunguna. Wasu kuma a na zargin sun karɓi kuɗin jama’a da sunansa ba tare da kai musu magungunan da su ka saya ba.
Mutanen da a ka kama sun haɗa da Muhammad Usman, Husaini Kabir, Hassan Kabir, Suleiman Salihu da Nura Garba.
Rundunar ta ce a na ci gaba da bincike domin gano wasu mutanen da ke da hannu a lamarin.
Ta kuma gargadi jama’a da su tabbatar da sahihancin magunguna masu sayarwa da hanyoyin biyan kuɗi kafin yin mu’amala, musamman a kafafen sa da zumunta.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
