Connect with us

News

Walƙiya Tayi Ajalin Mata Biyu, Ciki Har Da Mai Juna Biyu A Bauchi

Published

on

Lightning 1024x576

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane uku, ciki har da wata mata mai juna biyu da wata mai shayarwa, sakamakon walƙiya da ta auka wa wani gida a ƙauyen Gambiri da ke ƙaramar hukumar Bauchi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce guguwar hadari da walƙiya ta kashe mutane uku a ƙauyen.

DSS Ta Kama Jami’in Bogi Da Kayan Hukumar A Abuja

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Abubakar Hussain ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:29 na yammacin ranar Litinin, lokacin da walƙiyar ta auka wa ɗakin da waɗanda abin ya shafa suke ciki.

Ya ce an binne waɗanda suka mutu da misalin ƙarfe 11 na safe ranar Talata.

A cewarsa, ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu ita ce Hauwa Juli, wadda ta haihu kwanaki bakwai kacal kafin faruwar lamarin, tare da ’yarta mai suna Fatima.

Advertisement

Ya ƙara da cewa Habiba, wadda ke da juna biyu, ’yar uwar Hauwa Juli ce, yayin da jaririn da Hauwa ta haifa ya tsira daga lamarin.

Lamarin ya jefa al’ummar ƙauyen cikin jimami da alhini, yayin da aka dakatar da wasu harkokin zamantakewa da tattalin arziki saboda zaman makoki da mazauna yankin suka shiga.

 

 

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending