Connect with us

News

Rasuwar Ugboaja Babban Rashi Ne Ga Ƙungiyar NLC— Abbas Ibrahim

Published

on

70a20db1 19ca 4190 8d09 e41b7ffdedf3 1000x558 1

Ɗan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar Labour Party (LP), Kwamared Abbas Ibrahim, ya bayyana rasuwar Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Emmanuel Ugboaja, a matsayin babban rashi ga ƙungiyar ƙwadago da ma Najeriya baki ɗaya.

A cikin saƙon ta’aziyyar da ya aike wa Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ranar 27 ga Agusta, 2026, Abbas ya ce rasuwar Ugboaja ta girgiza harkar ƙwadago, duba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen kare haƙƙin ma’aikata da inganta walwalarsu.

Aƙalla Mutane 157 Ne Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Zaftarewar Ƙasa Da Ambaliyar Ruwa A Nepal

Ya ce marigayin ya kasance jagora mai hangen nesa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da adalci da kare muradun ma’aikatan Najeriya.

Abbas ya ce ƙwarewar Ugboaja a fannin shari’a ta taimaka matuƙa wajen ƙarfafa gwagwarmayar ƙungiyar ƙwadago da kuma kare muradun ma’aikata a lokuta da dama.

Ya tuna da haɗuwarsa da marigayin a ɗaya daga cikin tarukan horaswa na NLC na Harmattan School, inda ya ce kalaman ƙarfafawa da shawarwarin da ya bayar suka yi tasiri ga mahalarta taron.

Advertisement

“Ko da yake Ugboaja ya riga mu gidan gaskiya, amma ya bar tarihi mai kyau da kuma abubuwan tunawa da za su ci gaba da kasancewa a zukatan waɗanda suka yi hulɗa da shi,” in ji Abbas.

Tsohon Mataimakin Sakataren NLC na Jihar Kano ya buƙaci shugabannin ƙungiyar da mambobinta su yi haƙuri tare da ci gaba da tafiya a kan manufofin da marigayin ya tsaya kai da fata wajen ganin an cimma su.

Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokan aikinsa da daukacin al’ummar ƙwadago, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa da abokan aikinsa juriyar wannan babban rashi.

Abbas, wanda kuma tsohon Shugaban Majalisar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano ne, ya ce rasuwar Ugboaja ta haifar da wani gibi da zai yi wuya a cike a harkar ƙwadago ta ƙasar nan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending