News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Bai Wa Ɗalibai Kyautar DATA Kullum
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta fara bai wa ɗaliban Najeriya 100MB na data kyauta a kullum daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, domin samun damar shiga shafukan ilimi da manhajojin koyarwa da aka amince da su.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin ƙaddamar da shirin samar da damar shiga manhajojin ilimi ba tare da cajin data ba.
ZAƁEN 2027: CHRICED ta ƙarfafa ’yan jarida, CSOs kan kare haƙƙin jama’a
Ya ce shirin zai fara ne da ɗaliban makarantun sakandare na gwamnati da manyan makarantun gwamnati, kafin daga bisani a faɗaɗa shi zuwa sauran ɗalibai.
A ƙarƙashin shirin, kamfanonin sadarwa za su samar da 100MB na data kullum ga ɗaliban da suka cancanta, wadda za a yi amfani da ita wajen shiga shafukan ilimi da aka amince da su ba tare da biyan kuɗin data ba.
Alausa ya ce manufar gwamnati ita ce tabbatar da cewa babu ɗalibin da aka hana samun ingantaccen ilimi saboda rashin kuɗin data.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin ɗaukar matakan daidaita yadda yara ‘yan ƙasa da shekara 16 ke amfani da intanet, tare da tabbatar da cewa abubuwan ilimin da suke samu sun kasance masu aminci da dacewa.
A nasa jawabin, jami’in NCC, Ayuba Shuaibu, ya ce Hukumar Sadarwa ta Najeriya tare da Ma’aikatar Ilimi za su tantance shafukan da za a amince da su ƙarƙashin shirin.
Ya ce kamfanonin MTN, Airtel da Globacom na daga cikin masu gudanar da shirin, inda za su samar da data kyauta ga ɗalibai domin samun damar amfani da manhajojin ilimi.
