Connect with us

News

Ƙungiyar Magoya Bayan  Shugaba Tinubu Ta Zargi ’Yan Daba Da Hana Ta Kai Tallafi Ga Marasa Galihu A Bauchi 

Published

on

IMG 20261011 WA0012

Wata ƙungiyar siyasa mai suna Da Hannu Na, ƙarƙashin dandalin Arewa for Asiwaju, ta zargi wasu ’yan daba da kai wa tawagarta hari tare da tarwatsa shirin kai tallafi ga marasa galihu a Jihar Bauchi.

Shugaban ƙungiyar, Jamil Jadda Garko, ya ce ya tsira daga harin ne bayan jami’an tsaro sun shiga tsakani.

Dakarun Soji Sun Samu Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda 36

Lamarin ya faru ne a ƙarshen makon da ya gabata, bayan ƙungiyar ta gudanar da wani tattaki domin nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya samu halartar magoya bayansa daga jihohi bakwai na Arewa maso Yamma.

Masu shirya taron sun ce tattakin ya gudana daga yankin GRA zuwa filin wasa da kuma Double 4 Hall, ƙarƙashin rakiyar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Hukumar NSCDC da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC).

Sun bayyana cewa jami’an tsaron sun shiga tsakani cikin gaggawa, lamarin da suka ce ya taimaka wajen hana tashin hankalin rikidewa zuwa zubar da jini.

Advertisement

Ƙungiyar ta shirya ziyartar gidan gyaran hali, cibiyar gyaran hali da gidan marayu domin raba kayan tallafi a wani shirin jinƙai da aka shirya da sunan Shugaba Tinubu.

Sai dai masu shirya shirin sun yi zargin cewa wasu ’yan daba sun tarwatsa tawagarsu, lamarin da ya hana su kai tallafin da aka tsara.

Bayan faruwar lamarin, Garko ya yi barazanar kai ƙorafi ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da sauran manyan jami’an jam’iyyar APC domin neman a ɗauki mataki.

Sauran waɗanda ya ce za a sanar da su sun haɗa da Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nantawe, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Ibrahim Masari, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman, tare da shugabannin gwamnonin APC.

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa waɗanda ake zargi da kai harin suna da alaƙa da gwamnatin Jihar Bauchi, amma ba ta gabatar da wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da zargin ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar kan lamarin. Haka kuma, ba a tabbatar da ko akwai waɗanda suka samu raunuka ko kuma an kama wasu mutane dangane da zargin ba.

Advertisement

Masu shirya shirin sun ce sun je Bauchi ne a wani ɓangare na shirye-shiryen wayar da kan jama’a gabanin babban zaɓen 2027, tare da haɗa ayyukan siyasa da taimaka wa masu buƙatar agaji.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken dalilin arangamar ba, yayin da ake jiran ƙarin bayani daga hukumomin da abin ya shafa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending