News
Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka Ƴan ISWAP Sama Da 40 A Borno
Dakarun rundunar sojin sama ta Operation HADIN KAI sun kashe sama da ƴan ta’addar ISWAP 40 a wani samamen sama da suka kai kauyen Badu da ke ƙaramar hukumar Guzamala a jihar Borno.
Mai magana da yawun hedikwatar rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Maiduguri.
Dakarun Soji Sun Samu Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda 36
Ya ce samamen, wanda aka gudanar a ranar 10 ga Oktoba, ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan ISWAP na shirin kai hare-hare kan dakarun soji da ke aiki a yankin Sector 3.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa sama da ’yan ta’addar 40, ciki har da wani fitaccen kwamandan ISWAP, sun mutu sakamakon harin.
Ya ƙara da cewa an kuma lalata motoci biyu da babura kusan 20 da ’yan ta’addar ke amfani da su wajen sufuri, jigilar kayayyaki da kai hare-hare.
Goni ya bayyana cewa ’yan ta’addar na cikin rundunar Murabitun ta ISWAP, wadda ke gudanar da sintiri, tsara hare-hare da kuma ci gaba da ayyukan ta’addanci a yankin.
Ya ce lalata maboyar da kayayyakin yaƙin ’yan ta’addar zai raunana ƙarfinsu tare da kawo cikas ga shirye-shiryensu na kai hare-hare kan sansanonin soji da al’ummomin da ke kewaye.
Rundunar ta ce ana ci gaba da tantance illar da harin ya haifar, tare da jaddada aniyar ci gaba da haɗa hare-haren sama da na ƙasa domin kawar da ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.
