News
DSS Ta Kama Ɗan Abdulrasheed Maina Bayan Shekaru Shida Da Gujewa Jami’an Tsaro
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama Faisal Abdulrasheed Maina, ɗan tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho na Najeriya, Abdulrasheed Maina, bayan shafe shekaru yana gudun jami’an tsaro sakamakon karya sharuddan belinsa.
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa an kama Faisal a yankin Karsana da ke Abuja, bayan jami’an DSS sun samu bayanan sirri cewa ya dawo Najeriya a ɓoye.
DSS, Sojoji da ’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyar Bisa Zargin Sace ’Yan NYSC 20 A Imo
Bayan kama shi, an miƙa Faisal ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) domin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace a kansa.
Faisal ya tsere ne a shekarar 2020 bayan ya karya sharuddan belinsa a shari’ar da ake tuhumarsa da safarar kuɗi.
A watan Oktoban 2021, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari.
Sai dai a watan Nuwamban 2022, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rage hukuncin zuwa shekaru bakwai.
Kama Faisal na zuwa ne bayan shafe shekaru yana guje wa jami’an tsaro tun bayan da ya kauce wa shari’ar da ake yi masa.
-
News4 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News1 day ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News3 days ago
AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano
