Connect with us

News

Rushe Gidan Sha’aban: Lauya Ya Yi Zargin An Saɓa Wa Umarnin Kotu

Published

on

kotu

Lauyan tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Sabon Gari ta Zariya, Hon. Mahmoud Sani Sha’aban, ya zargi waɗanda suka rushe gidansa da amfani da umarnin kotu wajen aiwatar da abin da bai ƙunsa ba.

Lauyan, Barr. Abubakar M. Muhammad, ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan zaman shari’a a Kotun Majistare da ke Chediya, GRA, a Zariya, Jihar Kaduna.

Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

Ya ce sun halarci kotun ne domin neman ƙarin bayani kan rushe gidan, wanda ya ce suna zargin an yi shi ne ba tare da bin ƙa’idojin doka ba.

A cewarsa, rushe gidan ya faru ne a lokacin da ake ci gaba da takaddamar shari’a tsakanin Sha’aban da kamfanin Karim General Merchant kan gwanjon kadarorin tsohon ɗan majalisar, bisa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke.

Barr. Muhammad ya ce ɓangaren da ake ƙara ya nemi umarnin kotu domin shiga gidan, amma ya jaddada cewa umarnin bai ba da izinin rushe ginin ba.

Advertisement

“Umarnin kotun bai ambaci rushe kadarar ba. Sun yi amfani da wannan umarni wajen rushe gidan, shi ne dalilin da ya sa muka bayyana a gaban kotun a safiyar yau,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, bayan zaman kotun, lauyan kamfanin Karim General Merchant ya gabatar da takardar rantsuwar amsa ƙorafi (counter-affidavit).

Sai dai ya ce sun yi ƙorafi kan ƙarancin lokacin da aka ba su domin nazarin takardar, lamarin da ya sa Mai Shari’a Ibrahim Sa’idu ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2026.

Lauyan ya kuma bayyana cewa kotun ta bayar da umarnin dakatar da amfani da gidan har sai an yanke hukunci na ƙarshe kan takaddamar.

Ya ce suna tattara bayanai domin shigar da ƙara ta neman diyya kan rushe gidan, bisa zargin cewa an yi hakan ne ba bisa doka ba.

Ƙoƙarin jin ta bakin lauyan da ke wakiltar kamfanin Karim General Merchant bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending