News
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tsawaita dakatarwar da ta yi wa shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Bagwai da Bebeji da watanni uku.
Haka kuma, majalisar ta ƙara wa kwamitin wucin gadi da ta kafa wa’adin gudanar da binciken zargin karya ƙa’idojin gudanar da ayyuka da bin matakan da suka dace da ake yi wa shugabannin ƙananan hukumomin uku.
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
Wannan mataki ya biyo bayan ƙarewar wa’adin dakatarwar farko ta watanni uku da majalisar ta yi wa ciyamomin, tare da wa’adin da ta tanadar wa kwamitin domin gudanar da binciken.
A cikin wata sanarwa, sakataren yaɗa labarai na majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya ce an tsawaita wa’adin ne domin bai wa kwamitin damar kammala bincikensa, nazarin ƙorafe-ƙorafen da aka shigar kan shugabannin da kuma miƙa rahotonsa ga majalisar.
Sanarwar ta ƙara da cewa kwamitin, wanda aka kafa ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya samu ƙarin watanni uku domin kammala aikinsa.
Ana iya tuna cewa, tun a watan Augustan da ya gabata ne majalisar ta dakatar da Abubakar Mustapha na Rogo, da Dokta Alhassan Salisu na Bebeji da Bello Gadanya na Bagwai bayan amincewa da rahoton Kwamitin Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta kan hakan.
-
News21 hours ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News22 hours ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News6 days ago
An Kwantar Da Dalibai 64 A Asibiti Bayan Shan Maganin Cutar Bilharzia A Katsina

