News
Jami’an Soja Ya Samu Kyautar N500,000 Bayan Ya Ƙi Karɓar Cin Hanci

Rundunar Sojin Najeriya ta ba wani jami’in soja, Utim Terwase, kyautar Naira 500,000 bayan ya ƙi karɓar cin hancin da wani da ake zargi da garkuwa da mutane ya yi masa domin ya sake shi.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojan ya kama wanda ake zargin ne bayan ya yi ƙoƙarin tserewa, sai dai wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin ba shi kuɗi domin ya kuɓuta daga hannunsa.
Gwamnan Kano Ya Nemi Sauya Kwamishinan Ƴansanda Da DPO 18 Gabanin Zaɓen 2027 —Rahoto
An ce Terwase ya ƙi karɓar kuɗin, inda maimakon haka ya miƙa wanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike.
Mai magana da yawun rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Chinonso Oteh, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce Kwamandan Rundunar Soji ta 3, Manjo-Janar Maxwell Dangana, ne ya bayar da kyautar ta hannun Kwamandan Sashe na 6, Kanal Philimon Malgwi.
Oteh ya ce Dangana ya yaba wa sojan bisa gaskiya, amana da ƙwarewar aiki da ya nuna, yana mai cewa wannan hali ya nuna jajircewarsa wajen kiyaye ƙa’idojin aikin soja da fifita muradun ƙasa a kan son kai.
-
News3 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News3 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News13 hours ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
