News
Jami’an Ƴansanda Sun Kubutar Da Mutane 19 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kuɓutar da mutane 19, waɗanda suka haɗa da mata da yara, bayan shafe kwanaki 22 a hannun ’yan bindiga.
An kuɓutar da su ne a wani sansanin ’yan bindiga da ke kusa da ƙauyen Kungurmi a ranar 14 ga Nuwamban 2026.
Ba Ma Goyon Bayan Wata Jam’iyya Ko Ɗan Takara – Kungiyar ASUU
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan sace mutanen daga ƙauyen Tungar Haki da ke kusa da Wanke, a ƙaramar hukumar Gusau.
Ya ce tawagar haɗin gwiwa da ta ƙunshi jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar ’yan sanda, jami’an da ke fadar gwamnatin jihar, hukumar DSS da mafarauta ne suka gudanar da aikin. Dukkan mutanen 19 sun kuɓuta ba tare da sun samu rauni ba, kuma an mayar da su ga iyalansu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ahmad Muhammad Bello, ya yaba wa jami’an tsaron bisa jajircewa da haɗin gwiwar da suka nuna wajen kuɓutar da mutanen. Ya kuma tabbatar da aniyar rundunar na ci gaba da yaƙi da garkuwa da mutane da sauran laifuffuka, tare da kira ga jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai.
