News
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Jami’an tsaro a Pakistan sun kama wasu ’yan Najeriya 20 bisa zargin hannu a safarar miyagun ƙwayoyi a biranen Islamabad da Rawalpindi.
A yayin samamen da Rundunar Yaƙi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasar (ANF) ta gudanar, an kwato miyagun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 4.432, da suka haɗa da hodar ibilis, ƙwayar Ice da tabar wiwi.
Gobara Ta Tashi A Wata Kasuwa A Legas
Jaridar Pakistan Today ta ruwaito cewa rundunar ta gudanar da samamen ne bisa bayanan sirri, inda ta kai farmaki wasu wurare da ake zargin maboyar masu safarar ƙwayoyi ne.
Rundunar ta bayyana cewa waɗanda aka kama na zargin suna cikin wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke rarrabawa tare da sayar da su ga matasa, musamman ɗaliban makarantu da manyan makarantu.
Ta ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda ake zargin shugabannin ƙungiyar ne da kuma faɗaɗa bincike kan ayyukanta a Pakistan.
Samamen na daga cikin ƙoƙarin da hukumomin Pakistan ke yi na dakile safarar miyagun ƙwayoyi da kare matasa daga shiga harkar.
