Connect with us

Uncategorized

Ɗa Da Abokinsa Sun Shiga Hannun Ƴansanda  Bisa Zargin Shirya Garkuwa Da Kai Domin Karɓar Kuɗin Fansa Daga Hannun Mahaifinsa

Published

on

arrest 1000x600
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi ta kama wasu matasa biyu bisa zargin ƙulla makircin yin garkuwa da ɗaya daga cikinsu domin karɓar kuɗin fansar Naira miliyan 30 daga hannun mahaifinsa.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Fortune Onuoha da abokinsa, Godspower Nkwo, wanda aka fi sani da Hulk.

Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Joshua Ukandu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abakaliki, wadda ya aikewa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN).

A cewar sanarwar, mahaifin Onuoha ne ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda a ranar 31 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 10:30 na dare, inda ya bayyana cewa an yi garkuwa da ɗansa daga ɗakin kwanan ɗalibai da yake zaune a Ƙaramar Hukumar Ikwo ta jihar.

Mahaifin ya kuma shaida wa ’yan sandan cewa ya samu wasu bidiyoyi da saƙonnin murya da ke nuna ɗansa a ɗaure, yayin da waɗanda suka yi garkuwar ke neman a biya su Naira miliyan 30, tare da barazanar kashe shi idan ba a biya kuɗin ba.

Advertisement

Sai dai bayan samun rahoton, rundunar ta ƙaddamar da bincike na musamman, tare da tura jami’ai domin gano gaskiyar lamarin da kuma waɗanda ke da hannu a ciki.

Binciken ya kai ga cafke Onuoha da abokinsa, Nkwo, a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, lokacin da suka fito daga ɗakin da ake zargin suke ɓoye.

Sanarwar ta nakalto kwamishinar ’yan sandan jihar, Urunwa Okafor, tana gargaɗin jama’a kan ƙirƙirar garkuwa da kai ko yin ƙaryar sace mutum domin karɓar kuɗin fansa.

Kwamishinar ta ce irin wannan aika-aika na jefa iyaye da ’yan uwa cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, baya ga karkatar da hankalin jami’an tsaro daga tunkarar matsalolin tsaro na gaskiya.

Ta jaddada cewa ƙirƙirar garkuwa da kai da kuma yin ƙaryar sace mutum manyan laifuffuka ne da doka ta tanadi hukunci a kansu, inda ta buƙaci jama’a su guji aikata irin waɗannan laifuffuka, tare da bin hanyoyin da doka ta tanada wajen magance matsalolinsu.

 

Advertisement

VANGUARD

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending