Connect with us

News

Matasa Uku Sun Mutu Yayin Ƙoƙarin Ciro Waya Daga Masai A Zariya

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Matasa uku sun rasa rayukansu a unguwar Tudun Kusa da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, bayan sun shiga wani ramin masai domin ciro wayar salular da ta faɗa ciki.

Matasan da suka mutu su ne Najashi Haruna mai shekara 18, Abdullahi Adamu mai shekara 20 da Ashafa Jumare mai shekara 22.

Wasu Ɓatagari Ɗauke Da Makamai Sun  Farmaki Ayarin Kwankwaso Da Aminu Gwarzo A Bichi

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, inda matasan suka mutu ɗaya bayan ɗaya yayin ƙoƙarin taimaka wa juna.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa lamarin ya fara ne bayan wani mutum mai suna Murtala ya faɗa wa mutanen da ke kusa da shi cewa wayarsa ta faɗa cikin masan da ke gidansa.

Rahotanni sun ce mutumin ya yi alƙawarin ba da Naira 1,000 ga duk wanda ya iya shiga ramin ya ciro masa wayar.

Advertisement

Wannan alƙawari ne ya sa wasu matasa da ke kusa da gidan suka amince su shiga domin taimaka masa.

Mai Unguwar Tudun Kusa, Malam Jibrin Suleiman, ya shaida cewa yana gona lokacin da ƙaninsa ya kira shi da misalin ƙarfe 8:30 na safe, yana neman ya dawo gida cikin gaggawa.

Ya ce daga baya aka sanar da shi cewa wasu matasa sun shiga ramin masai domin ciro waya, amma lamarin ya rikide zuwa ajalinsu.

A cewarsa, matashi na farko da ya shiga ramin ya mutu, yayin da wani ya shiga domin ceto shi, amma shi ma bai samu damar fitowa ba. Daga bisani wani matashi na uku ya shiga domin taimaka wa abokansa, shi ma ya rasa ransa.

Wata mazauniyar yankin mai suna Fatima Haruna ta ce an ɗaure Najashi Haruna da igiya domin saukar da shi cikin ramin, amma igiyar ta tsinke, abin da ya sa ya faɗa ciki.

Ta ce wani matashi da ake yi wa laƙabi da Dille ya shiga domin ceto shi, amma shi ma bai fito ba. Wani na uku da ya yi ƙoƙarin shiga domin taimaka wa abokan nasa shi ma ya mutu.

Advertisement

Ana neman gano musabbabin mutuwar

Rasuwar matasan ta jefa mazauna yankin cikin alhini, musamman ganin yadda suka mutu yayin ƙoƙarin ceton junansu.

Fatima Haruna ta bayyana cewa an yi amfani da wani ƙarfe da ake kira ‘Kura’ wajen fitar da gawarwakinsu daga cikin ramin.

Ta ce abin da ya ba wasu mazauna yankin mamaki shi ne yadda ba a ga alamun najasa a jikin gawarwakinsu ba, duk da cewa an shafe sama da shekara 20 ana amfani da masan.

Wannan ne ya sa wasu mazauna yankin suka fara nuna shakku kan abin da ya haddasa mutuwarsu.

A nasa bangaren, Mai Unguwar, Malam Jibrin Suleiman, ya ce wasu dattawa sun nemi a yi amfani da kaza domin gwada yanayin da ke cikin ramin. Sai dai ya ce kazar ta firgita bayan an saukar da ita, lamarin da ya sa aka yi gaggawar fito da ita.

Advertisement

Duk da haka, har yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da ya haddasa mutuwar matasan ba.

‘Yan sanda sun fara bincike

Malam Suleiman ya tabbatar da cewa jami’an ’yan sanda sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru, inda suka fara tattara bayanai domin gudanar da bincike.

Ya ce mutuwar matasan, waɗanda dukkansu ba su yi aure ba, babban rashi ne ga iyalansu da al’ummar unguwar.

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun ziyarci yankin domin jajanta wa iyayen mamatan.

An gudanar da jana’izar matasan uku bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da ƙoƙarin jin ta bakin iyayensu bai yi nasara ba.

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending