Connect with us

Business

An dakatar da kamfanin jiragen sama na Dana Airlines daga aiki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH

 

 

Advertisement

 

Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya, ta soke lasisin kamfanin jiragen sama na Dana Airlines, daga tsakar daren ranar Laraba, 20 ga watan Yulin 2022.

Advertisement

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce Matakin ya biyo bayan binciken da hukumar ta gudanar kan karfin kudin gudanarwar kamfanonin jiragen sama, wanda kuma sakamakon binciken ya nuna cewa kamfanin Dana Air bai cika ka’idar da hukumar ke bukata wajen gudanar da jirage sama ba.

Mutum uku sun mutu a bikin hawan kaho

Advertisement

Dakatarwar ta yi daidai da tanadin sashi 35(2), 3(b) da (4) na dokar hukumar ta 2006, da kuma wani sashe na 1.3.3.3(a)(1) na dokar hukumar zirga-zirgar jiragen sama, ta 2015, suka tanada .

Hukumar kuma ta nemi fasinjoji wadanda su dakatarwar za ta fi shafa, da su fahimci dokar cewa an zartar da ita ne domin kare lafirsu, saboda a cewar hukumar ta fi bayar da muhimmanci kan lafiyar jirage fiye da komai

Advertisement

SOURCE BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending