News
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta’adda Suka Fitar.
Daga Yasir sani Abdullah fadar shugaban kasa ta yi martani kan bidiyon da yan ta’adda suka fitar na barazanar cewa za su tarwatsa Najeriya, tana cewa jami’an tsaro ba su ‘gaza ba kuma basira bata kare musu ba.
Yan ta’addan sun fitar da bidiyo inda suka yi barazanar cewa za su sace Shugaba Muhammadu Buhari.
Da ya ke martani, babban hadimin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa shugaban kasa ya yi dukkan abin da ya dace ya yi a matsayinsa na babban kwamandan tsaro ta hanyar karfafa musu gwiwa, siyan kayan aiki da makamai kuma yana tsammanin sakamako mai kyau.
Sanarwar da kakakin shugaban kasar ya fitar ta ce “yan ta’addan na amfani da farfaganda ne da tada fitina don tilastawa gwamnati ta amince da bukatunsu na siyasa kuma hakan ba sabon abu bane a duk duniya.
“Jami’an tsaro da dakarun kasar ba su gajiya ba kuma basira bata kare musu ba. Suna da shirinsu da hanyoyin aikinsu wanda ba za su nuna ba a kafafen watsa labarai.
Matsalolin da ake fuskanta kan yan ta’addan jirgin kasan yana da yawa:
Mataki irin yin ruwan wuta a dazukan inda suke zai biya bukatar masu ganin an dauki fansa amma me zai faru da wadanda aka sace? Ba su aikata laifi ba. Kawai sun shiga jirgi ne. “Jami’an tsaro ba zaune suke ba.
Sun san nauyin da ya rataya a kansu da abin da kasa ke tsammani daga gare su. Duk lokacin da za su yi wannan aikin suna fatan mutane su basu goyon baya.
“Ta’addanci matsala ne na duka duniya da ya dace kowa ya bada gudunmawa don yaki da shi – sojoji, farar hula da masu kamfanonin sadarwa.
Wannan shine kadai hanyar da ake iya cin galaba kan yan ta’adda a kowanne bangare na duniya.
“Don taimaka wa kasa a halin da ake ciki, ya zama dole kafafen watsa labarai su kara bada tallafi su yaki amfani da kafar intanet da dandalin sada zumunta da yan ta’adda ke amfani da shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
