News
Babban Kalubalen Da Na Fuskanta A Shekarun Aikina —CP Dikko
Daga kabiru basiru fulatan
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano mai barin gado, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ce babban kalubalen da ya fuskanta a Kano shi ne yadda ake bayar da belin wadanda suka aikata manyan laifuka bayan an kai su kotu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bankwana a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Dawowar Messi zuwa Barcelona ba abu ne mai yiwuwa ba yanzu
A ranar Laraba ne dai Kwamishinan zai yi ritaya daga aiki, sakamakon cikarsa shekaru 60 da haihuwa.
CP Dikko ya fara aiki a matsayin Kwamishinan ‘yan Sanda daga ranar 19 ga watan Fabrairun 2019.
CP Dikko ya kirayi Gwamnatin Kano da Kotuna a jihar da su duba yiwuwar aiwatar da abinda ya dace dangane da wannan kalubale na bayar da belin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka.
A cewarsa, “bai kamata a ce wani ya aikata babban laifi ba, kuma a sha wahalar kamo shi amma ya fi karfin doka ba.
Kazalika, CPn ya yi kira ga sauran jami’an rundunar, da su kasance masu bin dokar aikin na dan sanda a duk inda suka tsinci kansu.
Ana iya tuna cewa, a kwanan baya an samu dambarwa a Kano lokacin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yafe wa wasu mutane da aka kama bisa zarginsu da tayar da hankulan jama’a
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
