News
Ya Kashe Mahaifinsa Kan Kyautar Fili
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Wani matashi ya soka wa mahaifinsa wuka har lahira saboda mahaifin ya ki ba shi kyautar fili.
Matashin ya yi aika mahaifin nasa barzahu ne saboda mahaifin ya bukaci ya ba shi lokaci ya kasafta filin yadda zai yi wa sauran iyalansa adalci.
NLC ta soma gudanar da gagarumar zanga-zanga a Abuja
Matar marigayin ta ce: “Ya dade yana damun mijina shekara guda ke nan kan filin nan.
“A ranar Litinin ne maganar ta kai su ga musayar yawu, inda ya fusata ya zaro wuka ya sossoka wa mahaifin nasa a kai da wuya da hannaye da kafafunsa har ya mutu.
“Ihun da na yi ne bayan ganin abin da ya faru ya sanya ya tsere”, in ji ta.
A safiyar ranar Litinin ne al’ummar unguwar Masaka a Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa suka wayi gari da wannan danyen aiki na kisan magidancin da dansa ya yi.
Kanin wanda ake zargi da aikata ta’asar, kuma da na biyu ga margayin ya ce sun sanar da ’yan sanda, gawar mahaifin nasu kuma na ke ajiye a mutuware kafin kammala bincike
Daily Trust
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News13 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
