Connect with us

News

An tsinci gawarwakin ‘yan matan Saudiyya biyu a Australia. 

Published

on

Yan matan Saudiyya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

.

‘Yan sandan Australiya sun cika da mamaki bayan gano gawarwakin wasu matan Saudiyya biyu a cikin wani gida a birnin Sydney, wadanda ake kyautata zaton cewa an kai tsawon wata daya ba a gan su ba.

An gano gawarwakin matan da suka hada da Asra Abdullah Alsehli mai shekara 24, da Amaal Abdullah ‘yar shekara 23 a ranar 7 ga watan Yuni a wani gida da ke wajen birnin Canterbury.

Yada Bayanan ’Yan Ta’adda: Gwamnati Za Ta Kafa Wa BBC Da Trust TV Takunkumi

Advertisement

‘Yan sandan da aka kira zuwa gidan domin yin bincike sun ce ana kyautata zaton matan sun mutu ne tun a farkon watan Maris.

Sai dai ya zuwa yanzu masu binciken ba su kai ga gano dalili ba ko kuma yadda abin ya faru.

Matan wadanda ‘yan uwan juna ne sun koma Australiya daga Saudiyya a 2017 kuma ana kyautata zaton sun nemi mafaka, kamar yadda jaridar Sydney Morning ta ruwaito.

Sai dai ‘yan sanda sun ki tabbatar da hakan, inda suke cewa ba sa bayyana abubuwan da suka shafi matsayin zaman mutane.

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce za ta yi bincike domin gano ko matan sun tsere daga Saudiyya ne saboda cin zarafi ko kuma tsauraran dokokin kula da mata a cikin kasar. Sai dai ba wata hujja a kan hakan.

‘Yan sanda sun ce suna magana da iyalan matan, wadanda ke taimaka musu da bayanai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending