Connect with us

News

MDD ta buƙaci Poland ta daina nuna wa ‘yan Afirka masu neman mafaka wariya

Published

on

DAGA MUJAHID DANLAMI GARBA 

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bukaci Poland ta kawo karshen wariyar da take nuna wa ‘yan ci-rani.

Advertisement

Majalisar ta ce gwamnatin Poland na maraba da ‘yan Ukraine amma kuma sai ta garkame ‘yan asalin Gabas ta Tsakiya da Afirka da suka shiga kasar daga Belarus.

Mun kashe ‘yan bindiga 30 bayan harin da suka kai mana a Abuja – Sojin Najeriya

Advertisement

Wakilin musamman na MDD kan ‘yan ci-rani, Felipe Gonzalez, ya ce ana rike da su cikin yanayi na tagayyara a cibiyoyi da ake jidge baki ‘yan kasashen waje ba tare da ba su damar fita ba, yayin da suke dakon takardar izinin samun mafaka.

Mista Gonzalez ya ce bai kamata a garkame yara da mutane marasa karfi ba da nuna bambanci ko fifiko tsakanin ‘yan gudun hijira.

Advertisement

Wakilin BBC ya ce a cewar MDD, ‘yan Ukraine sama da miliyan 1.25 ne suka yi rajistar zama a kasar na wucin-gadi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending