News
Ba za mu sake tsawaita wa’adin rajistar katin zabe ba- INEC
Daga asim sani Abdullahi
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ba zata sake bude kofar mallakar katin zabe ba ga yan kasar, bayan cikar wa’adin ranar 31 ga watan Yulin 2022.
Kwamishinan Hukumar mai kula da sashen ilmantar da al’umma kan mallakar katin, Festus Okoye, ya fada wa BBC cewa sun bai wa jama’a duk irin lokacin da suke bukata don mallakar katin.
Akan haka yace ba za su sake tsawaita lokacin yankar rajistar ba, lura da yadda lokaci ke kure musu.
INEC ta ce tana so ta mayar da hankali ne ga sauran ayyukan da ke kan jadawalin zaben na 2023, kuma dole sai ta rufe yankar katin ne za ta iya samun ci gaba.
A ranar 28 ga watan Yuni ne hukumar zaben ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar zuwa ranar 31 ga watan Yulin 2022, bayan bukatar hakan daga bangarori daban-daban na kasar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
