News
An gurfanar da mutum 82 da zargin fyade a Afrika ta Kudu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu mutum 82 zasu gurfana gaban kotu a Afirka ta Kudu ranar Litinin a kan zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da yunƙurin kisan kai, da mallakar abubuwan fashewa, da kuma wasu laifukan da suka saɓawa dokokin shige da fice.
Ƴan sanda sun ce wadanda ake zargin basu rasa alaka da zargin aikata fyaɗen taron dangin da a ka yi wa wasu mata takwas a lokacin da suke daukar bidiyon wata waka.
Lamarin ya faru ne ranar alhamis a Krugersdrop, da ke yammacin Johannesburg.
Ana zargin ‘yan-sintiri da kashe malamin makarantar allo a Jihar Kano
Hukumomi sun ce matan da aka yi wa fyaden yan shekaru 19 ne zuwa 37.
Ɗaya daga cikin waɗanɗa abin ya shafa ta gaya wa wata jarida cewa, mutanen sun zo rataye da barguna da takunkumi a fuska, sannan suka tunkare su suna harba bindiga a sama.
Ta kara da cewa wani tsoho daga cikin wadanda ake zargin ya bai wa matasan da su yi musu fyaɗe sannan su yi musu sata.
Lamarin ya sa al’ummar Afirka ta Kudu sun kadu, inda wasu suka nanata kiraye-kirayen yin amfani da sinadarin kashe sha’awa ga wadanda aka kama da laifin aikata fyade.
