Gwamnonin jihohin Najeriya sun sake yin watsi da yunkurin fara cire kudaden Paris Club da suka kai dala miliyan 418 daga asusun tarayya don biyan wasu ‘yan kwangila.
Kungiyar gwamnonin ta aika wa gwamnatin tarayya wata wasika inda ta ce taɓa kudaden waɗanda suke ƙalubalantar batun a gaban kotu, karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin kasa.
An kai amarya gidan yari bisa dukan uwar-gida a kano
A wata wasika da ta aikewa gwamnatin Najeriya, ƙungiyar gwamnonin ta bayar da hujjar cewa duk wani yunƙurin daukr matakan fara zaftare kudaden, sun saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa, tun da ana shari’a a kan maganar.
Ta ce kuma tuni ma kotu Ƙoli ta fadi matsayinta a kan batun.
Shgaban ƙungiyar, kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya sanya hannu kan wasiƙar.
Sannan ƙungiyar gwamnonin na ganin lamunin da aka bayar tun da farko, wanda gwamnatin tarayya ta shiga tsakani, kuma ake maganar sake fara cire shi, an bayar da shi ne bisa kuskure ta hannun wasu ƴan kwangila.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba game da wasiƙar da ƙungiyar gwamnonin suka aike mata

