Connect with us

News

Nancy Pelosi ta ce Amurka ba za ta yarda China ta hantari Taiwan ba

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

 

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ce Amurka ba za ta lamunce wa China ta hantari Taiwan ba – bayan ziyarar da Ms Pelosi din ta kai ta fusata China.

 

Advertisement

Lokacin da ta yi magana a birnin Tokyo, na kasar Japan, Pelosi ta ce ba manufar ziyararta a kasashen Asia ba ne ta sauya matsayin da kasashe suke a kai ba.

Gwamnonin Najeriya sun sake watsi da yunkurin cire kudaden Paris Club na $418m

Yanzu haka dai sojojin China na gudanar da gagarumin atisaye a kusa da Taiwan, a matsayin martani kan ziyarar.

 

Wakiliyar BBC ta ce Ms Pelosi ita ce ‘yar siyasar Amurka mafi girman mukami da ta ziyarci Taiwan cikin shekaru 25, kuma ta yi watsi da zargin cewa wani kokari ne na bayar da kariya ga tsibirin.

 

Advertisement

China na kallon Taiwan a matsayin mallakinta, kuma tana iya yin amfani da karfi domin mayar da ita cikin ikonta, matukar bukatar hakan ta tashi.

 

 

BBC NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending