Connect with us

News

Ya Kashe Mahaifinsa Saboda Yi Wa Mahaifiyarsa Kishiya

Published

on

Gawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wani matashi mai suna Kazeem Muhammad ya tsere bayan kashe mahaifinsa saboda yi wa mahaifiyarsa kishiya shekara daya da ta gabata a garin Suleja da ke jihar Neja.

 

Advertisement

Dan uwan marigayin mai suna Isah ya shaida wa Aminiya cewa bayan ya kwada wa mahifin nasa falanki a ka, take Kazeem ya cika wandonsa da iska.

Ya ce, “Matashin na shaye-shaye sosai, don haka ya saba aikata abubuwan da ba su kamata ba.

Advertisement

Rushewar gini:Wani Dalibin sakandire ya rasa ransa a kano sakamakon ginin makarantarsu daya fado masa

“Ranar Laraba da safe ne sa-in-sa ta shiga tsakaninsa da mahifin nasa, sai ya kwada masa wani falankin katako da ke gurin, kuma take ya fadi, shi kuma ganin haka sai ya tsere.

Advertisement

 

“Mun kai shi asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma a nan take ya ce ga garinku nan,” inji dan uwan marigayin.

Advertisement

 

Ya kuma ce tuni suka sanar da hukumomin da suka kamata domin daukar mataki, sannan suka binne gawar mamacin.

Advertisement

 

Sai dai Rundunar ’Yan Sandan yankin ta ki cewa uffan a kan lamarin.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending