Connect with us

News

Najeriya Ta Tabarbare Fiye Da Yadda Take A 2015 – Sunusi

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

Mai Martaba Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya a Najeriya Muhammadu Sunusi na biyu, ya bayyana damuwa kan halin da Najeriya ke ciki, yana mai cewa, kasar nan ta tabarbare fiye da yadda take a shekarar 2015, lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki daga hannun Goodluck Jonathan.

Khalifa Sunusi na magana ne a wurin wani taro da Gidauniyar Akinjide Adeosun ta shirya kan sha’anin shugabanci a birnin Lagos.

A cewar sa “Wannan ita kadai ce kasar da ke samar da man fetur amma take kokawa a halin yanzu bayan da farashin man ya tashi sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.

Yace “Daukacin kudaden shigarmu ba za su iya biyan basukanmu ba.”

Khalifa Sunusi ya kuma yi gargadin cewa, abin da aka gani a 2015 nafila ne kan abin da zai faru a 2023, yana mai cewa, a halin yanzu Najeriya na fama da matsaloli da dama da suka hada da ta’addanci, hare-haren ‘yan bindiga da tsadar rayuwa da rashin tabbas kan farashin kudaden ketare.

Advertisement

Khalifan ya kuma ɗiga ayar tambaya yana mai cewa, ta yaya ne tarihi zai tuna shugaban kasa da gwamnoni da ministoci da suka shafe tsawon shekaru 8 kan karagar mulki?

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending