News
Yajin aikin ASUU: Dalibin jami’a ya koma siyar da shayi a Kano
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wani matashi dan aji biyu a karatun Digiri (200 Level) a jami’ar Yusuf Maitama Sule, mai suna Yusuf Auwal Barkum, ya fara sana’ar siyar da shayi a Unguwar Dawakin Dakata dake yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, sakamakon yajin aikin Ƙungiyar malaman jami’oi ta kasa (ASUU), wanda ya sanya Dalibai zaman gidan zaman dole.
Barkum ya bayyana cewa ya fara sana’ar siyar da shayi, taliyar yan yara da Kwai, kwanaki 10 da suka gabata, kuma tuni yanzu ya fara samun riba yana daukar dawainiyar kansa a abubuwa da dama.
Advertisements
