News
An kashe ‘yansanda da Indiyawa a wani harin bindiga a Kogi
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ‘yan bindiga sun kashe mutum shida a wani harin da suka kai kan motar Bas a jihar Kogi da ke arewa maso tsakiyar Najeriya.,
Mutanen da aka kashe sun haɗa da Indiyawa biyu da ke aiki a wani kamfanin gine-gine, da ‘yan sanda biyu da ke basu kariya da direbansu mutum biyu a harin na ranar Juma’a.
An kai harin ne a yankin Ajaokuta.
Ko a watan da ya gabata sai da ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sanda uku da masu aikin sa-kai biyar a wani hari ba-zata da suka kai a jihar.
A watan Yuni da Yuli ma sai da mayakan jihadi na IS suka hallaka ‘yan sanda hudu a hari kan ofisoshinsu biyu a yankin Okehi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
