Connect with us

News

Mutane Su Tashi Su Kare Kansu Daga ’Yan Ta’adda – Sheikh Jingir

Published

on

Sheikh Jingir

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah-Wa’ikatis-Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya yi kira ga al’umma su rika tashi tsaye domin kare kan su da garuruwan su daga hare-haren ta’addanci.

Advertisement

Shaihin Malamin ya yi kiran ne, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a garin Jos, inda ya ce bai kamata a ce ‘yan ta’adda 20 su shiga garin mutane dubu 1 su kama mutane su tafi da su ba tare da samun turjiyar mutanen garin ba.

Yan sanda sun kama wanda ake nema ruwa a jallo, Rasheed Okoilu, a Osogbo

Advertisement

Ya ce ya kamata mutane su hada kai, su tashi tsaye su kare garuruwan su, su kuma zakulo munafukan da ke cikin su.

Sheikh Sani Yahya Jingir, ya ce wasu bata-gari kuma makiya ci-gaban kasa a ciki da waje su na ta bata sunan Nijeriya a kan rashin zaman lafiya a kafofin yada labarai na yanar gizo.

Advertisement

Ya ce ya kamata masu kishin Nijeriya su fito su rika yin magana a kan abubuwan da suke faruwa, sannan ya nuna takaicin sa a kan faduwar darajar Naira.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending