Connect with us

News

Kasar Burkina Faso Ta Nemi Shawarar Najeriya Kan Yadda Zata Yaki Ta’addanci

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta nemi shawarar Najeriya kan yadda za ta yaki ta’addanci.

Babban hafsan sojin Burkina Faso, Kanar David Kadre, ya nemi shawarar a karshen mako a Abuja lokacin da ya ziyarci takwaransa na Najeriya, Janar Lucky Irabor, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito

Advertisement

Ya kuma yi nuni da cewa, ya je Najeriya ne domin halartar bikin yaye daliban kwasa-kwasai 30 na kwalejin tsaro ta kasa da kuma gabatar da yanayin tsaro a yankin yammacin Afirka.

Lauya Ya Maka Inec Kotu, Saboda Zargin Akwai Dungu Cikin Fam Ɗin Takarar Da Tinubu Ya Cike

Advertisement

“Na zo kuma game da ta’addanci da tada kayar baya a kasashenmu domin neman shawararku da gogewar ku tunda Najeriya ta tsunduma cikin yaki da wannan annoba,” in ji shi.

Kadre ya sake nanata bukatar kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da na Burkina Faso domin magance kalubalen ta’addanci da tada kayar baya.

Advertisement

A nasa bangaren Irabor ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa a tsakanin sojojin Afirka ta Yamma domin magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Ya taya Kadre, wanda tsohon dalibi ne a Kwalejin Tsaro ta kasa (NDC), Najeriya, murnar nadinsa.

Advertisement

Irabor ya ce Najeriya na alfahari da samun tsohon jami’in NDC ya zama babban hafsan tsaro na Burkina Faso, yana mai jaddada kudurinsa na raba ra’ayoyi da maziyartan.

“Babu shakka, yankin yammacin Afirka na fuskantar barazanar ta’addanci da tada kayar baya, kuma mun fahimci cewa, don magance wannan annoba, dole ne a samar da hadin gwiwar dukkanin kasashen yankin.

Advertisement

“Don haka na yi farin cikin karɓar ku kuma ina sanar da ku cewa za mu raba abubuwan da muka samu.

“Hakika za mu dauki matakin da zai tabbatar da cewa mun gyara dukkan batutuwa tare da tabbatar da cewa mun kawar da duk wani nau’in ta’addanci a yankinmu,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending