Connect with us

Sports

Benzema ya kama hanyar cin Ballon d’Or ne?

Published

on

 

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Advertisement

Karim Benzema ya ci gaba da fafutukar da yake yi ta cin lambar gwarzon kwallon kafa na duniya ta Ballon d’Or da kwallo ta 324 da ya ci wa Zakarun Turai, Real Madrid, a karawar da suka doke Eintracht Frankfurt suka dauki kofin Zakaran Zakaru na Turai, Super Cup a Helsinki ranar Laraba.

Kwallo ta biyu da Bezema ya ci bayan wadda David Alaba ya bude raga da ita, da ta sa aka tashi wasan na ranar Laraba 10 ga watan Agusta 2022, 2-0, ta sa ya zama na biyu a jerin ‘yan wasan da a tarihi suka fi ci wa Real Madrid kwallo.

Advertisement

Wannan kwallo ta sa ya wuce Raul ya zama na biyu a wasa 610 da ya yi wa Real Madrid bayan Ronaldo mai zunzurutun kwallo 450 a matsayin na daya.

Fafutukar samun Ballon d’Or

Ba tantama Benzema ya kasance a wannan kaka da ke neman zama mafi armashi a sana’arsa ta kwallon kafa inda ya ci Real Madrid kwallo 44 a wasa 46 ya taimaka wa kungiyar ta ci kofin Zakarun Turai da La Liga biyu.

Advertisement

Sai kuma wannan kofi na Zakarun Zakarun Turai, kuma bisa ga dukkan alamu yana kan hanyar ci gama da wannan zakakuranci ka kakkautawa.

Dan wasan mai shekara 34 wanda ya yi wa Real Madrid kyaftin a karawar ta Laraba a wannan makon aka jiyo shi yana cewa tsohon abokin wasansa Ronaldo ya taimaka masa a filin wasa da kuma wajen filin.

Advertisement

Amma kuma ya yarda cewa bayan tafiyar Ronaldon sai ya gano bakin zaren daga raga, inda ludayinsa ya hau kan dawo.

Yanzu dai da wannan kwallo da ya ci wadda ta daga shi ya shallake Raul a tarihin wadanda suka fi ci wa Real Madrid kwallo ya rabu a bayan Ronaldo.

Advertisement

Ya kasance yana samun yabo da jinjina kusan ta ko’ina tare da daka likkafa da matsayin kungiyarsa da kofunan da take ta zarewa, a iya cewa Benzema ya zama na gaba-gaba ma na gaban kawai da zai yi awon gaba da kyautar gwarzon kwallon duniya ta Ballon d’Or a watan Oktoba.

Daga cikin wadanda suke wadanda ke ganin kat ba wanda ya cancanci kyautar da Ballon d’Or akwai kociyan kungiyarsa Carlo Ancelotti wanda ya ce sun kai inda suka kai ni a yanzu saboda Benzeman.

Advertisement

Tsohon dan wasan Ingila Owen Hargreaves cewa ya yi in dai Benzema bai ci kyautar ba a yanzu to ba zai taba ci ba, ya ce bai ma ga dalilin da zai hana shi ci ba a wannan karon.

Shi ma tsohon dan wasan Real Madrid Steve McManaman yana da wannan ra’ayi , kuma ya kara da cewa Benzema ya cancanci komai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending