News
Wata sabuwa: Shekarau zai gana Tinubu a ranar Laraba
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Dan takarar shugaban ƙasar Nigeria a kakar zaben shekarar 2023 mai zuwa karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gayyaci tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, domin wata ganawa ta musamman a babban birnin tarayya Abuja, ranar Laraba mai zuwa, domin janyo shi cikin jam’iyyar APC.
Cikin wani Rahoto da Nasara Radio ta samu daga jaridar Daily Nigeria, ya nuna cewa Shekarau, wanda yake takarar Sanata a yankin Kano ta tsakiya, karkashin jam’iyyar NNPP, ya samu tayi daga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma dan takarar mataimakin shugaban Ƙasa na APC, Kashim Shettima.
Wata majiya ta bayyana cewa, akwai sabani da aka samu tsakanin Shekarau da jam’iyyar NNPP, saboda haka zai fice daga jam’iyyar nan bada dadewa ba, sai dai mai magana da yawunsa, Sule Ya’u Sule, ya karyata maganar, yana mai cewa a jirasu cikin mako guda domin jin matsayarsu a jam’iyyar.
