Connect with us

News

An kama wani mutum zai aika bindigogi Kano daga Abuja

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Kungiyar ‘yan sintiri a tashar motar Zuba da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ta kama wani mutum da bindigogi takwas da ya yi niyyar kai su Jihar Kano.

Jaridar DailyTrust ta ambato shugaban ‘yan sintirin da ke yankin, Yahaya Madaki, yana cewa lamarin ya auku a ranar Laraba.

Ya ce mutumin ya je tashar motar ne da misalin karfe biyu na rana inda yake neman motar da za ta je Kano don bayar da sakon.

Daga nan ne sai ya samu direban da ke lodi zuwa Kano ya mika masa sakon da aka sanya a kwali da kuma lambar wayar mutumin da zai kai wa sakon a Kano.

A cewar jaridar, an caji mutumin naira dubu 10 kudin dakon kayan, kuma nan take ya ciro ya bayar, daga nan ne sai direban motar ya nemi ya ji ko mene ne a cikin kwalin daga nan ne sai mutumin ya nemi ya tsere to amma an kama shi.

Advertisement

Yahaya Madaki ya ce ko da aka bude kwalin an ga bindiga samfurin AK-47 biyar, sai kananan bindigogi uku.

Yanzu haka mutumin na wajen ‘yan sanda inda suke gudanar da bincike a kan lamarin.

 BBC

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending