News
Ana zargin Yan shi,a da kone masallaci a unguwar dorayi babba
Daga Yasir sani Abdullahi
Rahotanni daga unguwar dorayi babba dake cikin karamar hukumar gwale sun tabbatar da cewa wasu Yan shi,a sun kone Wani masallaci
Shedun gani da Ido sun tabbatar wa da Jaridar bustandaily yadda lamarin ya faru inda suka ce lamarin ya farune a Daren ranar alhamis inda Yan shi,ar sukazo dauke da makamai da dama a hannuwan su Kuma take suka kunna wuta a masallaci
Malam Ahmad Dauda yace dama yan shi’ar sun dade da Sanar da cewa zasu kone masallacin tare da kashe Mai Unguwar yankin da Kuma liman Malam Saminu.
Rikici tsakanin Yan shi’a da al’ummar yankin ba sabon Abu bane a yankin Dorayi Babba.
Mun yi kokarin ji daga Bakin rundunar Yan sanda Kano a tabakin kakakinta ya ce zasu bincika domin Sanar da manema labarai cikakkiya gaskiya
