Connect with us

News

Shugabancin Nigeria ba,na malalaci bane cewar atiku Abubakar

Published

on

Atiku abubakar

Daga Yasir sani Abdullahi 

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria Kuma Dan takarar shugabancin kasa a jam,iyyar PDP atiku abubakar ya,ce shugabancin Nigeria Sam Sam bana malalaci bane Wanda baisan yadda kasar ke tafiya,ba

Atikun ya bayyana hakane lokacin da yake tattaunawa da gamayyar kafafen  yada labarai a jahar kano lokacin da ya kawo ziyarar kwanaki uku

 

Atiku Abubakar yace “Najeriya a yanzu bata da isassun ƴan sanda da zasu kare ƴan ƙasa, Najeriya na da al’umma da suka zarce miliyan ɗari biyu, amma ƴan sanda basu fi mutum dubu ɗari huɗu ba, a don haka bazasu iya tsare mutanen najeriya ba”.

 

Advertisement

“Shugabancin ƙasa kamar Najeriya ba na malalaci bane, lokacin ina mataimakin shugaban ƙasa, kowanne dare sai an kawo min rahoton bayanan tsaro na sirri, kuma sai na karance su, sannan na nemi Babban jami’in tsaro na ƴan sanda na tambayeshi me yasa abu kaza ya faru, sai a dauki matakin gaggawa,”. Inji Atiku Abubakar

Ya kara da cewa nigeria tana San shugaban kasar da zai jajirce wajan nuna jajircewar sa ga Al,umma Dan Basu tsaron da ya kamata domin magance matsalolin da ke addabar Yan kasar

Kuma ya zargi shugaban kasa muhammadu buhari da,gin daukar shawarar sa a lokacin shiyasa ya yabar jam,iyyar APC Kuma gashi kasar na bakutar irinsa  da zasu kawo matsalolin tsaro

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending